1 Thessalonians 3

1Saboda haka da muka kāsa ɗaurewa, sai muka ga ya fi kyau a bar mu a Aten mu kaɗai. 2Muka aiki Timoti, wanda yake ɗanʼuwanmu da kuma abokin aikin Allah a cikin yaɗa bisharar Kiristi, don yǎ gina ku yǎ kuma ƙarfafa ku cikin bangaskiyarku, 3don kada kowa yǎ raunana ta wurin waɗannan gwaje-gwajen. Kun sani sarai cewa an ƙaddara mu don waɗannan. 4Gaskiyar ita ce, saʼad da muke tare da ku, mun sha gaya muku cewa za a tsananta mana. Haka kuwa ya faru, kamar dai yadda kuka sani. 5Saboda wannan, saʼad da ban iya jimrewa ba, sai na aika domin in sami labarin bangaskiyarku, da fata kada yǎ zama mai jaraban nan ya riga ya jarabce ku, ƙoƙarinmu kuma yǎ zama banza.

Rahoton Mai Ƙarfafawa na Timoti

6Amma ga shi yanzu Timoti ya dawo mana daga wurinku ya kuma kawo labari mai daɗi game da bangaskiyarku da kuma ƙaunarku. Ya faɗa mana yadda kullum kuke da tunani mai kyau a kanmu, yadda kuke marmari ku gan mu, kamar dai yadda mu ma muke marmari mu gan ku. 7Saboda haka ʼyanʼuwa, cikin dukan damuwarmu da tsananinmu an ƙarfafa mu game da ku saboda bangaskiyarku. 8Gama yanzu tabbatacce muna da rai, da yake kuna nan tsaye daram a cikin Ubangiji. 9Wace irin godiya ce za mu yi wa Allah saboda ku a kan dukan farin cikin da muke da shi a gaban Allahnmu ta dalilinku? 10Dare da rana muna adduʼa da himma domin mu sāke ganinku, mu kuma ba ku abin da kuka rasa a bangaskiyarku.

11Yanzu bari Allahnmu da Ubanmu kansa da kuma Ubangijinmu Yesu yǎ shirya mana hanya mu zo wurinku. 12Ubangiji yǎ sa ƙaunarku ta ƙaru ta kuma yalwata ga juna da kuma ga kowa, kamar yadda tamu take muku. 13Bari yǎ ƙarfafa zukatanku har ku zama marasa aibi da kuma tsarkaka a gaban Allahnmu da Ubanmu saʼad da Ubangijimmu Yesu ya dawo tare da dukan tsarkakansa.

Copyright information for HauSRK